Najeriya-Kano

SERAP ta kai korafi MDD kan take hakkin tsohon sarki Sanusi

Batun tsige sarkin Kano Muhammadu Sanusi da gwamnatin jihar Kano a Najeriya ta yi ya dauki sabon salo, inda kungiyar kare hakkin dan adam da  zamantakewa ta SERAP, ta shigar da korafi gaban Majalisar Dinkin Duniya kan tauye masu hakkinsa na walwala.

Tubebben sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.
Tubebben sarkin Kano Muhammadu Sanusi II. AFP
Talla

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar, mataimakin daraktan kungiyar, Kolawole Oluwadare, ya bayyana cewa kungiyar ta aike da koke na gaggawa ga kwamitin Majalisar Dinkin Duniya da ke sa ido kan tsare mutane ba bisa ka’ida ba, kan tsarewa da cin mutuncin da ta ke zargin ana wa tsohon sarkin.

Korafin da kungiyar ta yi a ranar 11 ga watan Maris na wannan shekarar na cewa ci gaba da tsare sarki Sanusi na biyu ya saba wa dokar kasa, kuma take hakkinsa ne.

Ta ce ci gaba da tsare tsohon sarkin ya yin karan tsaye ne ga kundin tsarin mulkin Najeriya, tanaa mai kira ga Majalisar Dinkin Duniya ta shiga zancen ta wajen tuntubar gwamnatin jihar Kano da ma gwamnatin Najeriya kan batun.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI