Tarihin sabon sarkin Kano Aminu Ado Bayero

Sabon Sarkin Kano mai martaba Aminu Ado Bayero.
Sabon Sarkin Kano mai martaba Aminu Ado Bayero. Solacebase

An haif Alhaji Aminu Ado Bayero ne a shekarar 1961, yahyi makarantar firamare a Kofar Kudu dake Kano Municipal; daga nan ne ya garzaya Birnin Kudu na jihar jigawa a yanzu don makarantar sakandare.Sabon sarkin ya shiga jami’ar Bayero dake Kano, inda ya sami digiri a fannin koyon aikin jarida

Talla

Aminu Ado Bayero ya je makarantar koyon tukin jirgin sama dake Aukland a California ta kasar Amurka, ya kuma yi hidimar kasa a gidan talabijin NTA da ke garin Makurdi na jihar Binuwai, daga bisani aka dauke shi aiki a kamfanin zirga zirgar jiragen sama na Kabo Air.

A cikin shekarun 1990, mahaifin sabon sarkin, marigayi Alhaji Ado Bayero ya nada shi sarautar Dan Majen Kano, kuma Hakimin Dala.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya rike mukamin Dan Buran Kano, Turakin Kano da kuma Sarkin Dawakin Tsakar Gida, kafin mukamin Wamban Kano, sannan a shekarar 2019 aka nada shi Sarkin Bici, daya daga cikin masarautu 4 da gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ya kirkiro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.