Najeriya-Kano

Tsohon sarkin Kano Sanusi ya isa Legas

Alamu na nuni da cewa sarkin Kano a Najeriya da gwamnatin jihar ta tsige a wannan mako, Alhaji Muhammadu Sunusi na biyu ya sauka birnin Legas, inda ake zaton zai ci gaba da zama, akasin jihar Nasarawa kamar yadda hukumomi suka so tun da farko.

Tsohon sarkin  Kano, Muhammadu Sanusi II
Tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II http://newswirengr.com
Talla

Wata majiya mai karfi ta ce tun da safiyar wannan rana ta Alhamis ne sarkin Kanon na 14 ya baro jihar Nasarawa tare da wasu mukarrabansa zuwa birnin Legas a Najeriya, birnin da ya bukaci a kai iyalansa a ranar da aka tsige shi.

A ranar Litinin nan wannan makon ne gwamantin jihar Kano karkashin jagorancin gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta tsige sarki Muhammadu Sanusi, bisa zargin sa da ta yi da rashin mutunta hukumomi, kuma ta maye gurbinsa nan take da Alhaji Aminu Ado Bayero, da ga marigayi sarki Ado Bayero.

Sanarwar tsige shi da ta samu sa hannun sakataren gwamnatin jihar Kanon, Alhaji Usman Alhaji ta ce sai da gwamnatin jihar Kano ta tuntubi masu ruwa da tsaki kafin daukar matakin.

Matakin tisa keyar sarki Sanusi na Biyu zuwa jihar Nasarawa dai ya janyo cece kuce, inda wasu da dama ke diga ayar tambaya kan halarcin haramta wa wani zama a jiharsa sakamakon tsige shi.

Sai dai gwamnatin jihar Kano, ta ce ba ta da hannu a fitar da Sarkin daga jihar zuwa garin Loko a jihar Nasarawa.

Kwamishinan Shari’ar jihar, Barr. Ibrahim Mukhtar ya bayyana haka a zantawarsa da RFI Hausa, yana mai cewa, gwamnatin ta sauke Sanusi ne kawai daga kujerarsa amma ba ta da hannu game da fitar da shi daga jihar Kano.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI