Nijar

'Yan ta'adda sun kashe sojojin Nijar 9 a iyakar Mali

Wasu sojoji a yankin Sahel.
Wasu sojoji a yankin Sahel. REUTERS/Benoit Tessier/File Photo

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar sun ce wasu 'yan ta’adda da ke dauke da makamai sun hallaka sojojin kasar guda 9 a harin da suka kai musu a Ayorou dake Yankin Tillaberi kusa da iyakar Mali.

Talla

Kamfanin dillancin labaran Faransa yace bayan harin, anyi nasarar kashe daukacin maharan sakamakon harin saman da aka kai musu a yankin dake na nisar kilomita 200 daga birnin Yammai.

Jamhuriyar Nijar na cigaba da fuskantar ayyukan Yan ta’adda dake kai hare hare kan dakarun ta akan iyakar kasar da Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.