Wasanni-Kwallon kafa

An dakatar da gasar firimiya ta Ingila saboda coronavirus

Hukumar dake kula da kwallon kafa a Ingila ta sanar da dakatar da duk wasannin kwallon kafa har zuwa ranar 3 ga watan Afrilu saboda yaduwar cutar coronavirus.Sanarwar da hukumar ta bayar yace dakatarwar ta shafi daukacin wasannin firimiya da an league-league da gasar mata.

Gasar frimiya na kasar Ingila
Gasar frimiya na kasar Ingila Glyn KIRK / IKIMAGES / AFP
Talla

Hukumar tace za’a cigaba da gudanar da wasannin daga ranar 4 ga watan gobe idan masu kula da harkokin lafiya sun amince da samun cigaba wajen yaki da cutar.

An kuma baiwa kungiyoyi shawarar kaucewa taron jama’a ko kuma taro tsakanin ‘yan wasa da ‘yan kallo da kuma ziyarar baki zuwa filayen wasanni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI