Afrika

Ghana ta sanar da samun mutane 2 da suka kamu da cutar coronavirus

Hukumomin kasar Ghana sun sanar da samun mutane biyu dake dauke da cutar coronavirus daga cikin wasu matafiya da suka koma gida.Ministan lafiya Kwaku Agyemang Manu ya ce cikin mutanen biyu daya ya fito ne daga kasar Norway daya kuma daga Turkiya, kuma yanzu haka an killace su inda ake kula da su.

Kwayar cutar Coronavirus
Kwayar cutar Coronavirus (Photo By BSIP/UIG Via Getty Images)
Talla

Gwamnatin ta bukaci jama’a da su dinga kare kan su wajen kaucewa cudanya da jama’a da kuma yawan tsaftace hannayen su.

Tun kafin samun masu dauke da cutar, shugaban kasa Nana Akufo-Addo ya sanar da ware Dala miliyan 100 domin daukar matakan ko ta kwana dangane da barazanar cutar.

Yayin da yake jawabi ga al’ummar kasar, shugaban ya baiwa jami’an gwamnati umurnin dakatar da tafiye tafiye zuwa kasashen waje.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI