Kotu ta bada umurnin gaggauta sakin tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi
Wata babbar kotu a Najeriya ta baiwa gwamnatin kasar umurnin gaggauta sakin tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi da ake tsare da shi a garin Awe dake Jihar Nasarawa bayan tube shi daga karagar mulki.
Wallafawa ranar:
Alkali Anwuli Chikere na kotun ne ya bada umurnin sakin sa sakamakon karar da lauyoyin tsohon Sarkin suka shigar inda suke kalubalantar ministan shari’a da Sufeto Janar na Yan Sanda da kuma Daraktan hukumar DSS dangane da tsare Sanusi.
Lauyoyin sun kuma bukaci gabatar da takardar karar ga wadanda ake tuhuma ta wasu hanyoyi idan an gaza samun su domin mika su takardar gayyata.
A ranar litinin ne gwamnatin Jihar Kano ta bada umurnin sauke tsohon Sarkin abinda ya sa jami’an tsaro suka dauke shi daga fadar sa zuwa garin Loko dake Jihar Nasarawa kafin a sauya masa wurin zaman zuwa Awe.
Tuni gwamnatin Jihar Kano ta nada Aminu Ado Bayero a matsayin sabon Sarkin Kano.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu