Amurka ta kafa dokar ta baci kan Coronavirus
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Sakamakon cutar makoshi ta Coronavirus dake ta barna a kasashen duniya da shafar tattalin arziki, kasashen duniya na ta bayyana irin illar da cutar ta haifar masu, Shugaban Amurka Donald Trump ya aiwatar da dokar ta baci,bayan da dokar nan ta hana duk wani matafi daga yankin Turai sauka kasar ta soma aiki a Amurka.
Haka zalika Shugaban Venezuela Nicolas Maduro ya aiwatar da dokar ta baci biyo bayan gano wasu mutane biyu dake dauke da cutar Coronavirus.
Iran ta ce, a cikin sa’o’i 24 da suka shude, Coronavirus ta kashe mata mutane 85, abin da ya sa alkaluman mamata a kasar suka kai 514 kamar yada ma’aiktar kiwon lafiyar kasar ta sanar.
Yanzu haka jumullar Iraniyawa dubu 11 da 364 aka tabbatar sun harbu da cutar mai sarke hanyar numfashi.
Da dama daga cikin ‘yan siyasar Iran sun kamu da cutar
Ita kuwa gwamnatin Faransa ta sanar da rufe cibiyoyin karatu har tsawon makwanni biyu a wani mataki na dakile yaduwar wannan annoba a kasar.
Hukumomin a Faransa ta bakin Ministan kiwon lafiya mutane 8.00 ne suka kamu cikin sa’o’I 24 wanda yawan su ya kai 3.661,mutane 79 suka riga mu gidan gaskiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu