Burkina Faso

Burkina Faso ta dau matakan kare kai daga Corona

Kasuwar Banfora, a kasar Burkina Faso
Kasuwar Banfora, a kasar Burkina Faso Wikipedia

A jiya juma’a hukumomin Burkina Faso sun sanar da gano wani mutum dake dauke da cutar Coronavirus, adadin mutanen dake dauke da cutar a kasar yanzu haka uku a cewar Ministan kiwon lafiya Dokta Claudine Lougue.

Talla

Ranar litinin da ta gabata ne aka gano mutanen farko ma’aurata da suka fito daga Faransa ,wanda bayan gwaji aka kuma garzaya da su zuwa asibiti .

Daga ranar laraba da ta gabata dai ne hukumomin kasar suka sanar da haramta duk wani gangami ko taruruka a sassan kasar.

Burkina Faso mai yawan al’uma kusan milyan 20 ta sanar da ware kusan bilyan 9 na cfa kwontakoncin Euros milyan 13 domin samar da magugunan kariya don hana kamuwa da cutar Coronavirus.

Wasu daga cikin kasashen yammacin Afrika da suka hada da Nijar,Mali,Benin sun sanar da daukar matakan da suka dace wajen bayar da kulawa ta musaman ga matafiya daga kasashen da aka gano bulluwar wannan cuta ta Coronavirus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI