Darajar naira ya tashi bayan fargabar da aka samu
Rahotanni daga Najeriya sun darajar kudin kasar na naira ya tashi akan dalar Amurka sakamakon fargabar da aka samu saboda rade radin cewar Babban Bankin Najeriya zai karya darajar kudin.
Wallafawa ranar:
A makon jiya darajar naira ya fadi kasa daga naira 368 akan dala guda zuwa naira 366 sakamakon faduwar farashin mai saboda illar da cutar coronavirus ta yiwa harkokin kasuwanci da zuba jari.
A ranar alhamis an sayar da Dalar Amurka guda akan naira 400, yayin da a kasuwar bayan fage aka sayar da ita akan naira 430.
Amma jiya juma’a an sayar da Dalar Amurka akan naira 375.
Takaddama tsakanin Saudi Arabia da Rasha ta sa Saudi da kawayen ta kara yawan man da suke fitarwa zuwa kasuwannin duniya, abinda ya sa farashin ya fadi daga Dala 53 kowacce ganga zuwa Dala 33.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu