Afrika

Wasu Turawa biyu sun tsere daga hannun yan ta'adda

Turawan da suka tsere daga hannun yan ta'adda jim kadan da isowar su Bamako
Turawan da suka tsere daga hannun yan ta'adda jim kadan da isowar su Bamako Minusma

Majalisar Dinkin Duniya tace dakarun ta sun gano wasu ‘yan kasashen Turai biyu da aka sace a shekarar 2018 a Burkina Faso kuma suna nan da ran su a kasar Mali.

Talla

Wani jami’in Majalisar dake aiki da MINUSMA ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewar, dakarun su sun gano ‘dan kasar Italiar tare da matar sa ‘yar kasar Canada kusa da garin Kidal, inda aka yi garkuwa da su.

Majiyar tace tuni aka dauke su zuwa tashar jiragen Bamako kuma suna cikin koshin lafiya.

Mahamat Saleh Annadif, shugaban dakarun Majalisar yace da misalin karfe 3 na ranar jiya dakarun Majalisar suka sanar masa da gano mutanen, bayan sun tsere daga inda aka tsare su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI