Faransa

Faransawa na cikin fargaba kan zaben kananan hukumomi

A Faransa ga alama abubuwa na shirin tsaya cik duk da yake a yau lahadi ake gudanar da zaben wakilan kananan hukumomi da na magadiyan gari, biyo bayan bulluwar cutar Coronavirus a kasar.

Wasu daga cikin ruhunan zabe a Faransa
Wasu daga cikin ruhunan zabe a Faransa RFI/Alexis Bedu
Talla

Hukumomin kasar dake ci gaba da shan suka daga wasu yan siyasa da suka bukaci a dage zabukan sabili da wannan cuta,sun bukaci kowane dan kasar dake da katin zabe ya isa rufar zabe da bairon sa a hannu.

Yan kasar na ci gaba da nuna dar-dar musaman ganin ta yada ake ta radin-radin cewa somin tabi ne lamarin da ya shafi cutar Coronavirus a Faransa.

Yan takara sama da dubu 900 ne ke sa ran kasancewa daga cikin mutanen da za su dahe kujerun wakilan kananan hukumomi dubu 500.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI