Coronavirus

Halin da nahiyar Afrika ta shiga saboda annobar mura

Kasar Morocco ta fadada matakin haramta zirga-zirga tsakaninta da karin kasashe 25, bayan irin matakin, na farko da ta dauka kan kasashe 5 masu fama da annobar Coronavirus da suka hada da China, Spain, Italy Faransa da kuma Algeria.

Wasu jami'an lafiyar Kenya bayan aikin tsaftace yankin da aka samu mutumin da ya soma kamuwa da cutar Coronavirus a garin Rongai dake gaf da birnin Nairobi. 14/3/2020.
Wasu jami'an lafiyar Kenya bayan aikin tsaftace yankin da aka samu mutumin da ya soma kamuwa da cutar Coronavirus a garin Rongai dake gaf da birnin Nairobi. 14/3/2020. REUTERS/Baz Ratner
Talla

Wasu daga cikin karin kasashen 25 da Morocco ta haramta shige-da fice tsakaninta da su sun hada da Austria, Brazil, Chadi, Masar, Denmark da Jamus.

Yanzu haka dai gwamnatin Moroccon ta rufe makarantu gami da haramta tarukan sama da mutane 50, bayan gano mutane 18 da suka kamu da cutar murar a kasar.

A Libya dake fama da rikici kuwa gwamnatin kasar da majalisar dinkin duniya ke marawa baya tace daga gobe litinin za ta rufe iyakokinta na kasa tsawon mako 3, saboda dakile yiwuwar bullar annobar ta Coronavirus a kasar.

A Senagal jiya asabar Shugaban kasar Macky Sall ya sanar da haramta taruka, rufe makarantu da kuma soke bukukuwan ranar samun ‘yancin kan kasar na 4 ga watan Afrilun dake tafe, bayan tabbatar da rahoton mutane 21 a kasar da suka kamu da murar ta coronavirus.

A Afrika ta kudu kuma jami’an lafiya sun ce kawo yanzu mutane 38 annobar ta shafa.

Rwanda, Namibia, da Jamhuriyar Congo gami da Sudan dukkaninsu a karshen mako suka tabbatar da bullar annobar murar cikinsu.

Tuni dai wannan annoba ta bulla a kasashen, Najeriya, Togo, Kamaru, Gabon Ghana, da Burkina Faso da Kenya. Sauran kasashen sun hada da Mauritania, Habasha, Tunisia da kuma Masar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI