Duniya

Majalisar Dinkin Duniya ta damu da halin da ake ciki dangane da Corona

Ga baki daya jama'a sun kauracewa fitowa sabili da cutar Coronavirus
Ga baki daya jama'a sun kauracewa fitowa sabili da cutar Coronavirus TANG CHHIN Sothy / AFP

Kasashen Faransa da Spain sun sanar da karfafa matakan kariya don hanna yaduwar cutar Coronavirus,wacce yanzu haka ke ci gaba da yaduwa kamar wutar daji a kasashen Duniya.

Talla

Kasar Spain na a mataki na biyu a Turai inda cutar ta fi muni, alkaluma na bayyana cewa mutane dubu5. Da 753 ne aka gano sun kamu da ita da kuma dake mataki na hudu a Duniya da aka kuma samu mutuwar mutane 183.

Firaministan kasar Pedro Sanchez ya gayyaci yan kasar da su kaucewa duk wasu taruruka ko wani yawon shakatawa.

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa daya daga cikin jami’an ta dake aiki a birnin Geneva ya kamu da cutar Coronavirus,yayinda Birtaniya inda aka gano cewa mutane 1.140 sun kamu da cutar ta nuna jan kaffa wajen daukar matakan da suka dace don hana yaduwar cutar,kasar da mutane 21 suka rasa rayukan su bayan kamuwa da Coronavirus take cikin shirin wajen haramta tarurruka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.