Fashewar tukwanen iskar gas ce ta janyo iftila'i a Lagos - NNPC
Kamfanin man fetur na NNPC a Najeriya ya ce tukwanen iskar gas ne musabbabin fashewar da ta auku a Lagos a ranar Lahadi, lamarin da ya yi sanadin asarar rayukaKamfanin ya yi wannan bayani ne a wata sanarwa da ta samu sa hannun jami’in hulda da jama’arsa, Kennie Obateru, inda ya ce wata babbar mota ce ta doki tukwanen gas, lamarin da ya kawo fashewar.A yankin Abule-Ado na jihar Lagos a Najeriya ne wannan iftila’i ya auku da sanyin safiyar Lahadi.Mutanen yankin da dama, cikinsu har da dalibai suka makale a cikin baraguzan gini sakamakon rugujewar da gidaje suka yi biyo bayan fashewar.Ga rahoton Bashir Ibrahim Idris.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
NIGERIA-BASHIR IBRAHIM-1.30sec-2020-03-16
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu