Najeriya

Mayakan Boko Haram sun kashe sojojin Najeriya 6

Sojojin Najeriya 6 sun mutu bayan wani harin kwanton bauna da wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne suka kai musu a garin Banki da ke jihar Borno a arewa maso –gabashin kasar.

Shugaban Boko Haram  Abubakar Shekau, a tsakiyar mayakansa.
Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau, a tsakiyar mayakansa. News Ghana
Talla

Majiyoyin soji sun tabbatar da cewa harin ya auku ne kusa da marabar garin na Banki.

Kamar yadda jaridar Premium Times da ake wallafawa a kasar ta ruwaito, cikin sojojin Bataliya na 151 da harin ya rutsa da su, akwai masu mukamin saja guda 2, sai masu igiya daya daya 2, sai kuma mutum 2 marasa igiya.

Raahotanni daga garin na Banki na cewa, maharan sun yi wa sojin Najeriya shigan bazata ne da muggan makamai masu sarrafa kansu, inda suka ‘ci karensu ba babbaka’.

Garin Banki yana da nisan kilomita 130 a kudu maso gaabashin jihar Borno, kuma baya ga ‘yan asalin yankin, garin ya kasance gida ga ‘yan gudun hijira dubu 45, wadanda rikicin Boko Haram ya daidaita.

Rundunar sojin kasar ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance game da wannan lamari ba.

Harin na wannan Lahadin dai shine na baya bayan nan a cikin jerin hare hare da kungiyar Boko Haram ke kai wa a garuruwan jihar Borno.

Rikicn Boko Haram ya yi sanadin mutuwar mutane dubu 30, ya kumaa raba miliyoyi da muhallansu a jihohin Adamawa, Borno da Yobe, a cewar Majalisar Dinkin Duinya.

Rundunar sojin Najeriya ta yi kokari wajen takaita ayyukan Boko Haram a tsakanin jihohin arewa maso gabashin kasar. Sai dai kungiyar tana da karfin kai hare –hare kan fararen hula da sojoji da sauran jami’an tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI