Kamaru

Jam'iyyar adawa a Kamaru ta zargi gwamnati da yunkurin kashe jagoranta

Jam’iyyar Maurice Kamto da ke adawa da shugaba Paul Biya na Kamaru, ta zargi gwamnati da yunkurin kashe jagoranta, to sai dai ministan sadarwa ya musanta wannan zargi.

Maurice Kamto, jagoran 'yan adawan Kamaru
Maurice Kamto, jagoran 'yan adawan Kamaru REUTERS/Zohra Bensemra
Talla

A ranar juma’ar da ta gabata, wasu mutane uku a cikin farin kaya, sun kusanci kofofin motar da ke dauke da jagoran ‘yan adawa Maurice Kamto lokacin da yake ziyara a yankin Arewacin kasar, bayan da aka tabbatar da cewa sun dauki hotunan motocin da ke yi wa dan adawar rakiya.

A cikin wannan yanayi ne jami’an da ke kare lafiyar Kamto suka cafke biyu daga cikin mutanen kamar dai yadda Sakataren Jam’iyyar MRC Roger Justin Noah ya bayyana.

Bayan gudanar da bincike an gano cewa daya daga cikin mutanen na dauke da bindiga, kafin daga bisani a tabbatar da cewa mutanen biyu jami’an tsaron gwamnati ne, lamarin da ya sa jam’iyyar ta bijiro da wannan batu da ke cewa gwamnatin ce ta tsara hallaka jagoranta.

To sai dai ministan sadarwa, Rene Emmanuel Sadi a nasa martani, zargin magoya bayan Kamto ya yi da gallazawa jami’an tsaro a lokacin da suke kan aikinsu, kuma wanda ake cewa an kama da makami yana kan aikinsa ne sannan ba ya da niyyar hallakar Maurice Kamto.

Kamto, shi ne ya zo na biyu a zaben shugabancin kasar na 2018, to amma jam’iyyarsa ta yanke shawarar kaurace wa zaben ‘yan majalisar dokoki da na kananan hukumomi da aka yi cikin watan fabarairun da ya gabata, kuma kafin nan jagoran ‘yan adawar ya share tsawon watanni 8 tsare a gidan yari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI