Najeriya

Likitoci sun fara yajin aiki a Najeriya

Wasu likitoci a dakin tiyata a tarayyar Najeriya
Wasu likitoci a dakin tiyata a tarayyar Najeriya premiumtimesng.com

Yayin da kasashen duniya ke kokarin daukar matakan kariya tareda nazari kan yadda za su shawo kan cutar Coronavirus, likitocin a babbaan birnin Tarayyar Najeriya sun sananr dafara yaajin aiki a Talatar nan.

Talla

Kungiyar likitocin Najeriya, reshen Abuja sun sanar da fara wannan yajin aikin ne sa’a guda bayan hukumomin kasar sun sanar da mutum na 3 da ya harbu da cutar ta Coronavirus a birnin Lagos.

Likitocin sun ce sai da suka yi nazari sosai kan barazanar da bangaren lafiya ke fuskanta a wannan yanayi na annobar coronavirus, kuma sun yi la’akari da yanayin da suke aiki a ciki da ma na marasa lafiyar da suke kula da su kafin su cimma matsaya kan yajin aikin.

A wata sanarwa da ta samu sa hannun shugabanta, Roland Aigbovo, kungiyar ta ce matakin yajin aikin ya biyo bayan rashin biyan su albashinsu ne da hukumomin birnin Tarayyar suka yi na tsawon watanni biyu.

Mr Aigbovo ya ce wannan al’amari ya jefa likitocin cikin wani mawuyacin hali, kuma duk da kashedi da da suka yi ta yi, hukumomin ba su yi komai game da hakan ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI