Najeriya ta jingine batun rancen dala miliyan 22.7
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta sanar da dakatar da batun karbar rancen dalar Amurka 22.7 kamar yadda ta bayyana tun da farko kan abin da ta kira ‘ matsalar da tattalin arzikin duniya ya shiga.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Ministar kudin kasar Zainab Ahmed ce ta sanar da haka a wani jawab da ta yi a babban birnin Tarayyar kasar Abuja.
Bular cutar coronavirus a karshen shekarar da ta gabata ta jefa tattalin arzikin duniya cikin mawuyacin hali, lamarin da ya sa yanzu haka farashin gangar danyen mai ya yi mummunan faduwar da ba a taba gani ba a tun shekarar 2016.
Ganin cewa tattalin arzikin Najeriya ya ta’allaka ne kacokan kan man fetur da dangoginsa, wannan faduwa da farashinsa ya yi a kasuwannin duniya ya sa dole a samu matsala wajen aiwatar da kasafin kudin, la’akari da cewa an tsara kasafin kudin ne bisa yakinin za a sayar da gangar danyen mai kan dala 57, kuma yanzu farashin ya koma kasa da dala 30.
Ministar ta ce gwamnatin Najeriya ba za ta yi daukin karbar wannan rance ba, ko da ma majalisar dokokin kasar ta amince da hakan a yanzu.
Zainab Ahmed ta ce gwamnatin za ta jinkirta ta ga yadda al’amura ke ci gaba da gudana a kasuwannin duniya, kuma da zarar an samu ci gaba, za ta waiwayi batun karbar rancen.
Ta ce gwamnatin kasar za ta ci gaba da mayar da hankaalinta ne kan kudirinta na fadada hanyoyin samun kudin shiga, maimakon dogaro kacokan kan danyen mai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu