Najeriya-Coronavirus

Najeriya ta tabbatar da samun mutum na 3 da Coronavirus.

An samu mutum na uku daya kamu da COVID 19 a Najeriya.
An samu mutum na uku daya kamu da COVID 19 a Najeriya. (Photo By BSIP/UIG Via Getty Images)

Hukumomin Najeriya sun sanar da cewar an samu mutum na 3 da ya kamu da cutar coronavirus da ke ci gaba da hallaka rayuka a kasashen duniya.

Talla

Kwamishinan lafiyar Jihar Lagos Akin Abayomi ya sanar wa manema labarai samun mutumin, wanda aka ce ‘yar Najeriya ce mai shekaru 30 da ta komo gida daga Birtaniya ranar 13 ga watan nan.

Abayomi yace bayan ta ga alamun cutar sai ta killace kan ta, kana gwajin da aka mata ya tabbatar da cewar tana dauke da cutar.

Mutane 3 ya zuwa yanzu aka tabbatar sun kamu da cutar da suka hada da ‘dan kasar Italia da ya shiga kasar da ita da mutumin da yayi mu’amala da shi, sai kuma wannan da ta koma gida daga Bitaniya.

Yan Najeriya na ta kir aga gwamnatin kasar da ta hana baki daga kasashen da aka samu cutar zuwa cikin ta kamar yadda kasashen duniya suka yi, amma ya zuwa yanzu gwamnati bat ace komai ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.