Nijar

Sojin Nijar sun kashe mayakan Boko Haram 50

Gwmanatin Jamhuriyar Nijar ta ce dakarun kasar sun kashe mayakan Boko Haram sama da 50 a gumurzun da aka yi tsakanin dakarun da kuma ‘yan ta’addar cikin daren 15 zuwa wayewar garin 16 ga wannan wata.

Sojin Nijar
Sojin Nijar Ludovic MARIN / POOL / AFP
Talla

Sanarwar da ma’aikatar tsaron kasar ta fitar ta ce mayakan na Boko Haram a cikin motoci fiye da 20, sun kai hari kan barin sojin garin Toumour da ke jihar Diffa, to sai dai sojojin sun mayar masu da zazzafan martani tare da kashe akalla 50 daga cikin ‘yan bindigar.

Sakamakon tsanantar fadan, sauran mayakan na Boko Haram sun arce, to sai dai wata bataliyar sojin kundumbala ta yi masu kofar raga lokacin da suka isa gabar tafkin Chadi, kuma a wani lokaci ne aka kashe adadi mai yawa na ‘yan bindigar.

To sai dai sanarwar ma’iakatar tsaron ta ce jami’in kasar daya ya samu rauni a lokacin fadan, yayin da

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI