Kamaru ta rufe iyakokinta saboda Coronavirus
Kamaru inda mutane 10 ke dauke da kwayar cutar ta Coronavirus ta sanar da matakan dakile yaduwar annobar da suka shafi ciki da wajen kasar.
Wallafawa ranar:
Matakan sun hada da rufe makarantu, iyokoki na kan tudu, na ruwa da na sama.
Sai dai ‘yan asalin kasar ta Kamaru da ke zaune a kasashen ketare na da damar komawa gida idan suna bukatar hakan.
A lokacin da yake bayyana matakan ta kafar yada labaran gwamnati ta CRTV, Firaminista Joseph Dion Ngute yace shugaban Paul Biya ya bayar da umarnin cewa matakin rufe iyakokin kasar ta Kamaru zai soma aiki ne daga ranar laraba 18 ga wannan wata na maris.
Zalika an dakatar da tashi da saukar jiragen sama daga kasashen ketare illa kawai jiragen saman daukar kaya da kuma jiragen ruwan dakon muhimman kayayyaki, su ma suna da damar gudanar da irin wannan jigilar ce a cikin yanayi na tsari.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu