Afrika-WHO

Kasashen Afrika sun damu dangane da cutar Coronavirus

Mahamadou Issifou Shugaban jamhuriyar Nijar
Mahamadou Issifou Shugaban jamhuriyar Nijar ©RFI

A nahiyar Afirka, kafin karfe 12 na daren da ya gabata an tabbatar da cewa Coronavirus ta kama mutane 463, kuma yanzu haka gwamnatoci a nahiyar sun fara daukar tsauraran matakai don hana yaduwar cutar.

Talla

Wasu daga cikin kasashen da yanzu haka aka tabbatar da cewa cutar bata bullu ba, hukumomi na ci gaba da daukar matakan da suka dace don dakile ko kuma hana yaduwar Coronavirus a cikin su.

A jamhuriyar Nijar duk da cewa ba a samu koda mutum daya da ya kamu da cutar ba, amma a jawabinsa ga al’ummar kasar cikin daren iya talata, shugaban kasar Issifou Mahamadou ya sanar da matakin rufe iyakokin kasar na sama da na kasar daga ranar 19 ga wannan wata, tare da rufe makaruntun Boko baki daya daga ranar  juma’a.

Jamhuriyar Nijar ta sanar da daukar matakai dangane da coronavirus

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.