Coronavirus ta fara lakume dimbin rayuka a Afrika
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce, cutar Coronavirus ta kashe mutane 17 cikin sa’o’i 24 da suka gabata a nahiyar Afrika.
Wallafawa ranar:
Cutar na ci gaba da yaduwa a nahiyar Afrika, inda kawo yanzu aka tabbatar da bullarta a kasashen 33 na nahiyar.
Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce, an tabbatar da mutane 633 da suka kamu da Coronavirus a kasashen Afrika 33.
Kodayake cutar ba ta yi mummunar yaduwa ba a Afrika kamar yadda ta yi a wasu nahiyoyin duniya kamar Asiya da Turai.
Kasar Masar ce ke kan gaba wajen yawan masu dauke da Coronavirus a Afrika, inda take da mutane 210 da suka kamu da ita. Sai Afrika ta Kudu mai mutane 116, yayin da Algeria ke da mutane 75.
Najeriya ta tabbatar da mutane takwas da suka kamu da cutar ta Coronavirus.
Wannan annuba ta kashe fiye da mutane dubu 8 a sassan duniya kawo yanzu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu