Bakonmu a Yau

Farfesa Usman Muhammad kan gargadin WHO game da Coronavirus a Afrika

Sauti 04:02
Shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus dan kasar Habasha.
Shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus dan kasar Habasha. Fabrice COFFRINI / AFP

Yanzu haka dai nahiyar Afrika na shirin fuskantar mummunan yanayi dangane da cutar Coronavirus dake ci gaba da haddasa hasarar rayuka a duniya, kamar yadda shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus yayi gargadi.Kan wannan gargadi kuma Mahamman Salisu ya tattauna da Farfesa Usman Muhammad, shugaban Tsangayar huldar diflomasiya ta kasa da kasa a Baze University dake Abuja Najeriya, kan yadda masana ke kallon rashin maida hankali da ake zargin kungiyar tarayyar Afrika bata yi wajen yaki da cutar.