Afrika

Coronavirus ta shafi kasashen Afrika sama da 30

Jamhuriyar Nijar da Chadi sun zama kasashen Afrika da a baya bayan nan suka tabbatar da rahoton bullar cutar Coronavirus cikinsu, alkalumman dake nuna cewar annobar na ci gaba da yaduwa a nahiyar.

Shugaban hukumar lafiya ta duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus.
Shugaban hukumar lafiya ta duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus. ©REUTERS/Denis Balibouse
Talla

A daren alhamis da ya gabata, ma'aikatar lafiyar Jamhuriyar Nijar ta tabbatar da rahoton bullar annobar a kasar, inda wani ma’aikacin kamfanin sufuri mai shekaru 36 ya kamu.

A Najeriya kuma hukumomin kasar sun bayyana samun karin wasu mutane 4 dauke da cutar ta coronavirus abinda ya kai adadin mutanen da suka kamu a kasar zuwa 12.

Kawo yanzu hukumomin lafiya sun tabbatar da bullar wannan annoba a kasashe 34 dake Afrika, inda hukumar lafiya ta duniya WHO ta tabbatar da cewar mutane 633 da suka kamu da Coronavirus a kasashen nahiyar, wasu 17 kuma suka mutu.

Har yanzu dai cutar ba ta yi mummunar yaduwa ba a Afrika kamar yadda ta yi a wasu nahiyoyin duniya kamar Asiya da Turai da kuma Iran dake yankin gabas ta tsakiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI