Mali

'Yan ta'adda sun kashe sojin Mali 30

Wasu daga cikin sojojin Mali
Wasu daga cikin sojojin Mali Michele Cattani/AFP/Getty Images

Rahotanni daga Mali na cewa wasu da ake zargin mayaka masu ikirarin jihadi ne, sun kai wani kazamin hari a sansanin sojin kasar, inda nan take suka kashe sojoji 30 da jikkata wasu 5.

Talla

Majiyoyin samun labarai a Bamako na cewa, an kai wannan kazamin harin ne a sansanin sojin Mali da ke Tarkint a arewacin Gao.

Tun da farko rundunar sojin ta ce, tana fuskantar barazanar za a kai wa sansaninta hari a Tarkint.

Tun a ranar Alhamis ne, Firaministan kasar, Boubou Cisse ya sanar cewa, duk da barazanar da ake samu ta fannin tsaro, za a ci gaba da zaben wakilan majalisar kasar da aka shirya gudanarwa.

Zagaye na farko na wannan zabe, zai gudana ne a ranar 29 ga wannan wata, yayin da zagaye na biyu zai gudana a ranar 19 ga watan gobe.

Firaministan ya kara da cewa, lallai za a yi wannan zaben wakilan majalisa ko da cutar Coronavirus ta bulla a kasar.

Tun shekara ta 2012  masu ikirarin jihadi da karfin tsiya ke kashe mutane a kasar ta Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.