An dakatar da sufurin jiragen kasa a Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammdu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammdu Buhari. ng.gov.jpg

Hukumar kula sufurin jiragen kasa ta Najeriya ta sanar da dakatar da jigilar fasinjoji a fadin kasar, kuma dakatarwar za ta fara aiki ne daga ranar Litinin, 23 ga watan Maris da muke ciki.

Talla

Kakakin hukumar, Yakub Mahmood ya ce hukumar ta dau wannan mataki ne da zummar dakile yaduwar cutar coronavirus.

Wannan dakatarwar za ta shafi jiragen da ke jigilar fashinjoji kan layin dogo na Abuja zuwa Kaduna, Lagos zuwa Ogun da ma Lagos zuwa Ibadan da ake gwajinsa a halin yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.