Coronavirus

Gungun fasinjojin Gambia sun tsere daga inda aka killace su

Wani yankin Dakar babban birnin kasar Senegal dake makotaka da kasar Gambia. 18/3/2020.
Wani yankin Dakar babban birnin kasar Senegal dake makotaka da kasar Gambia. 18/3/2020. REUTERS/Zohra Bensemra

Jami’an tsaro da hukumomin lafiyar Gambia sun dukufa wajen neman wasu mutane 14 da suka tsere daga otal din da aka killace su, bayan zargin cewa sun kamu da cutar murar Coronavirus.

Talla

Gungun marasa lafiyar dai na daga cikin fasinjoji 32 da suka sauka a Banjul babban birnin kasar ta Gambia daga Birtaniya tun a larabar da ta gabata, wadanda a take aka killace su.

MInistan lafiyar Gambia Ahmadou Lamin Samateh yace ta karfin tsiya fasinjojin suka balle kofar shigar otal din kafin samun nasarar tserewa.

A talatar da ta gabata Gambia ta bada rahoton farko na bullar murar ta coronavirus a kasar bayan gano wata mata da ta kamu bayan isa kasar daga Birtaniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI