Ministoci 4 sun kamu da cutar coronavirus a Burkina Faso

Wasu 'yan kasar Burkina Faso rufe da fuskokinsu domin kare yaduwar annobar murar Coronavirus a birnin Ouagadougou. 16/3/2020.
Wasu 'yan kasar Burkina Faso rufe da fuskokinsu domin kare yaduwar annobar murar Coronavirus a birnin Ouagadougou. 16/3/2020. AFP

A Burkina Faso, ministoci 4 na cikin wadanda suka harbu da cutar coronavirus a baya bayan nan, inda yanzu haka hukumomi suka sanar da mutuwar mutane biyu sakamakon cutar.

Talla

Sanarwai da ma’aikatun harkokin kasashen waje, cikin gida, ilimi da ma’adinai suka fitar, sun tabbatar da cewa ministocinsu sun harbu da cutar COVID 19 a kamar yadda sakamakon gwajin da aka yi musu ya nuna.

Burkina Faso na da mutane 64 da suka kamu da wannan cuta, inda 29 daga cikinsu mata ne, yayin da 35 maza.

A ranar Juma’a, a kasar ta sanar da rufe iyakokinta na kasa da sama, sannan ta sanya dokar takaita zirga zirga da ta fara aiki daga Asabar, 21 ga watan Maris da zummar yaki da wannan annobar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.