Guinea

Masu bore sun kone gine-ginen gwamnati gabannin zaben raba gardama

Daya daga cikin gine-ginen da masu bore suka kone a kasar Guinea Conakry, yayin rikici kan zaben raba gardamar yiwa kundin tsarin mulki kwaskwarima.
Daya daga cikin gine-ginen da masu bore suka kone a kasar Guinea Conakry, yayin rikici kan zaben raba gardamar yiwa kundin tsarin mulki kwaskwarima. AFP / CELLOU BINANI

A yayinda kasashe ke fafutukar dakile annobar murar Coronavirus dake yaduwa kamar wutar daji, a kasar Guinea, ofisoshin gwamnati, makarantu da kuma wani caji ofishin ‘yan sanda masu bore suka lalata bayan cinna musu wuta.

Talla

Lamarin ya biyo bayan rikicin siyasar da ya tashi gabannin zaben raba gardamar da aka tsara zai gudana a yau lahadi, kan yiwa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima, matakin da ‘yan adawa ke zargin shugaba Alpha Conde da yunkurin yin amfani da damar wajen yin tazarce, duk da karewar wa’adin mulkinsa.

Zaben raba gardamar na Guinea na zuwa ne a dai dai lokacin da kasashe ke daukar matakan hana tarukan jama’a saboda dakile yaduwar annobar murar Coronavirus da kawo yanzu ta kama mutane 2 a kasar ta Guinea.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.