Coronavirus

Sama da mutane dubu 1 sun kamu da murar Coronvirus a Afrika

Annobar murar Coronavirus ta shafi kasashen nahiyar Afrika 40 daga cikin 54.
Annobar murar Coronavirus ta shafi kasashen nahiyar Afrika 40 daga cikin 54. AFP / Pius Utomi Ekpei

Alkalumman hukumomin lafiya sun ce zuwa jiya asabar adadin wadanda suka kamu da cutar Coronavirus a Afrika ya haura dubu 1.

Talla

A ranar asabar din kasar Angola ta sanar da mutum na farko da ya kamu da cutar, abinda ya sanya a yanzu adadin kasashen nahiyar Afrika da wannan annoba ta shafa kaiwa 40 daga cikin 54.

A karon farko annobar murar ta halaka rai a Jamhuriya Congo, yayinda wasu karin mutane 2 suka mutu a Burkina Faso.

A Somalia gwamnati ta sanar da bude iyakokinta na sama ne tsawon kwanaki 2, domin baiwa ‘yan kasar dake kasashen ketare damar komawa gida.

Yanzu haka dai Burkina Faso ke kan gaba a Afrika wajen fama da annobar murar, bayan halaka mata mutane 3 da kuma shafar wasu 64.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.