Najeriya-Coronavirus

Atiku ya musanta zargin 'dansa ya yada Coronavirus

Alhaji Atiku Abubakar tsohon mataimakin shugaban Najeriya.
Alhaji Atiku Abubakar tsohon mataimakin shugaban Najeriya. REUTERS/Nyancho NwaNri

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya yi watsi da zargin cewar ‘dan sa ya san ya na dauke da cutar coronavirus amma ya yi ta yawo ya na bazawa mutane.

Talla

Atiku ya ce babu gaskiya dangane da wanan labari, domin ‘dan nasa ya koma Najeriya ne a ranar 17 na wannan watan daga Switzerland bayan ya halarci taron kasuwanci a Faransa da Switzerland.

Sanarwar da tsohon mataimakin shugaban kasar ya gabatar ta ce ‘dan na sa ya ziyarci Lagos shi kadai, ba tare da iyalan sa ba, inda ya halarci taron mutane 6, ya kuma kwana a gidan sa kafin da safe ya hau jirgin Aero zuwa Abuja.

Acewar Atiku Abubakar ‘dan na sa na sanye da kyallen da ke rufe fuska domin kariya tun da ya koma Najeriya, kuma ya shaidawa hukumar yaki da cututtuka ranar 18 ga wata cewar ga kasashen da ya fito domin a gwada shi.

Sanarwar ta ce an yiwa dan gwaji ranar 19 ga wata inda aka gano yana dauke da cutar ranar 20 ga wata, inda ya killace kan sa domin kare iyalan sa.

Tsohon mataimakin shugaban na Najeriya Atiku Abubakar ya ce babu gaskiya cewar ya halarci Sallar Juma’a ko kuma wani taro har zuwa lokacin da aka dauke shi zuwa asibitin Gwagwalada ranar 20 ga wata inda ake kula da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI