An killace Gwamnan Bauchi saboda Coronavirus
Wallafawa ranar:
Gwamnan Jihar Bauchi a tarayyar Najeriya Senator Bala Muhammad, ya kebe kansa daga haduwa da jama’a sakamakon haduwarsa da dan tsohon mataimakin shugaban Nigeria Atiku Abubakar wanda aka tabbatar ya harbu da kwayar cutar COVID 19.
Rahotanni sun ce Gwamnan na Bauchi ya gana da Muhammed Atiku Abubakar yayin shigarsu jirgin sama daga Lagos zuwa Abuja inda har suka yi musafaha da juna.
Wata sanarwa daga Babban hadimin Gwamnan a fannin yada labarai Muktar Gidado, ta bayyana cewa ya-zuwa yanzu, Gwamna Bala Muhammad bai nuna wata alamar kamuwa da cutar ba, to amma bisa shawarar hukumar dakile yaduwar cututtuka ta Nigeria, Gwamnan zai ci gaba da kasancewa a killace don gudun yada cutar.
Rahotanni sun ce ana binciken jinin Gwamnan na Bauchi don tabbatar da matsayinsa kan cutar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu