Najeriya-Coronavirus

Adadin masu dauke da Coronavirus ya karu zuwa 42 a Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta sanar da samun sabbin mutane 2 da suka kamu da cutar coronavirus ko kuma COVID-19 abinda ya kawo adadin wadanda suka kamu da cutar zuwa 42.

Wasu jami'an lafiya da ke kula da masu dauke da cutar Coronavirus.
Wasu jami'an lafiya da ke kula da masu dauke da cutar Coronavirus. REUTERS/Zohra Bensemra
Talla

Hukumar yaki da cututtuka a kasar ta ce mutanen biyu sun fito ne daga Lagos da Ogun, kuma daya daga cikin su ya koma kasar ne daga tafiyar da ya yi zuwa kasar waje, yayin da na biyu kuma ya samu cutar ne daga mu’amala da wani mai dauke da ita.

Hukumar ta ce wannan ne karo na farko da aka samu wani da ke dauke da cutar da ya sanyawa wani tun bayan samun cutar a watan jiya.

Wannan labari ya nuna cewar Lagos ke sahun gaba wajen yawan masu dauke da cutar, inda take da 29 yanzu haka, sai kuma Abuja mai mutane 7 sai kuma Jihar mai Ogun wadda ke da mutane 3.

Jihohin Ekiti da Oyo da Edo na da mutuum guda guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI