Faransa-Afrika

Faransa za ta agazawa kasashen Afrika don yakar Coronavirus

Gwamnatin Faransa ta bayyana shirin kaddamar da agaji domin taimakawa kasashe matalauta musamman wadanda ke nahiyar Afirka domin kare kan su daga cutar coronavirus da ke cigaba da lakume rayuka.

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa.
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa. REUTERS/Pascal Rossignol
Talla

Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Yves Le Drian ya bayyana haka yayin da ya ke jawabi a zauran Majalisar Dokokin kasar, inda ya ke shaida musu irin matakan da gwamnatin kasar ke dauka don dakile yaduwar wannan cuta ta coronavirus daga yankunan kasar musamman wadanda basu kamu ba ya zuwa yanzu.

Le Drian ya ce wadanan yankuna da yanzu haka basu harbu da cutar ba, na iya zama babbar barazana ga Faransa gobe.

Alkaluman da aka tattara sun bayyana cewar mutane sama da 2,000 suka kamu da cutar coronavirus a Afirka, wadanda suka hada sassan nahiyar baki daya, kuma ya zuwa yanzu an bayyana mutuwar mutane 59.

Masana sun dade suna gargadin kasashen Afirka cewar, ya dace su dauki matakin kariya saboda tabarbarewar harkokin kula da lafiyar su da kuma yawan jama’ar da ke zama a matsugunai marasa inganci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI