Coronavirus ta kashe fitaccen mawakin Afirka Manu Dibango
Fitaccen mawakin Afirka, haifaffan kasar Kamaru, Manu Dibango ya rasu yau talata yana da shekaru 82 sakamakon kamuwa da cutar coronavirus.
Wallafawa ranar:
Mai kula da harkokin yada labaran mawakin Thierry Durepaire yace mawakin ya rasu ne yau da safe a wani asibiti dake wani Yanki na birnin Paris.
Wani sako da aike da shi ta kafar shafin san a Facebook ya tabbatar da rasuwar mawakin da kuma bayyana shirin masa jana’iza ba tare da gayyatar jama’a ba.
Tuni fitattun mutane suka fara tsokaci dangane da mutuwar mawakin wanda yayi fice akan wakar sa ta ‘Soul Makossa’ a shekarar 1972.
Cikin wadanda suka bayyana alhinin su dangane da mutuwar mawakin sun hada da fitaccen mawakin Senegal Youssou Ndour da ministan al’adun Faransa Frank Riester.
A shekarar 2009 mawakin ya zargi Michael Jackson da sace masa wakokin sa guda biyu, daga bisani mawakan biyu sun sasanta ba tare da zuwa kotu ba.
An dai haifi Emmanuel N’Djoke Dibango da aka fi sani da Manu Dibango a ranar 12 ga watan Disambar shekarar 1933 a Kamaru, kuma yayin da ya cika shekaru 15 mahaifin sa ya tura shi Faransa domin zama injiniya, abinda ya bashi damar karatu da kuma rungumar waka.
Lokacin da ya rungumi waka mahaifin sa ya katse kudin tallafin da yake bashi na karatu, abinda ya say a koma Brussels inda ya samu aikin waka, kuma acan ya gamu da matar da ya aura Marie-Josse da aka fi sani da Coco da kuma jagoran tawagar mawakan sa Joseph Kabasle.
Bayan ya koma gida ya kuma kwashe shekaru yana jagorancin wani gidan shakatawa, Manu Dibango ya koma Paris Faransa a farkon shekarar 1960, inda ya shiga tawagar mawaki Dick Rivers kafin a shekarar 1972 ya rera wakar Soul Makossa wadda ta sa shi fice a duniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu