Masar

Human Rights ta zargi jami'an tsaron Masar ta azabtar da yara

Wasu jami'an 'yan sandan Masar rike da wata karamar yarinya da suka kama.
Wasu jami'an 'yan sandan Masar rike da wata karamar yarinya da suka kama. AFP

Kungiyar Kare Hakkin Bil Adama ta Human Rights Watch ta zargi jami’an tsaron kasar Masar da azabtar da kananan yaran da suke tsarewa a gidajen yari.

Talla

Zargin na kunshe ne cikin rahoton da kungiyar ta fitar a baya bayan nan kan halin da ake ciki dangane da batun na kare hakkin dan adam a kasar ta Masar.

Rahotan mai shafuka 43 da kungiyar tare da takwararta ta Masar suka fitar, ya bayyana yadda aka azabtar da yara akalla 20 masu shekaru tsakanin 12 zuwa 17.

Kungiyoyin sun bukaci kasashen Amurka da Faransa da wasu kasashen Turai da su daina saidawa Masar makamai saboda lamarin.

Rahoton kungiyoyin ya zargi ma’aikatar tsaron cikin gidan Masar, da sojoji da hannu wajen kame kananan yara ba bisa hakki ba, batar da su, yi musu dukan kawo wuka da kuma azabar da su da wutar lantarki, da sunan tuhumarsu da alaka da kungiyoyin ‘yan ta’adda, ko kuma akan manufa ta siyasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI