Nijar

'Yan bindiga sun sace mutum 9 tare da hallaka wasu 4 a Madarunfa

Bandits place N1m levy on Katsina village to avoid attack
Bandits place N1m levy on Katsina village to avoid attack Daily Trsut

Rahotanni daga garin rurruka na yankin Gabi a Gundumar Madarunfa na cewa ‘yan bindiga sun kai hari daren jiya litinin, inda suka afkawa garin. Wasu ganau sun shaida cewa a wannan karon maharan sun yi wa garin kofar rago ne ba tare da sun yi amfani da Babura ba.

Talla

Alkaluma na nuni da cewa akalla mutane hudu ne ‘yan bindigar suka kashe, tare da yin awon gaba da wasu mutanen tara, duk da cewa a wannan karo ba su yi nasarar tafiya da dabbobi ba.

Wannan dai shi ne hari mafi muni da ‘yan bindigar wadanda ke tsallakowa daga jihar Zamfara a tarayyar Najeriya suka kai a garin na Rurruku a yankin Gabi a baya-bayan nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.