Sudan

Ministan tsaron Sudan ya rasu a Juba

Ministan Tsaron Sudan Laftanar Janar Jamal al-Din Omar ya rasu a Juba dake Sudan ta kudu inda yake halartar taron zaman lafiya tsakanin bangaren gwamnati da Yan Tawayen kasar.

Taron zaman lafiya na Sudan ta kudu
Taron zaman lafiya na Sudan ta kudu REUTERS/Jok Solomun
Talla

Kakakin rundunar sojin kasar Amer Mohammed al-Hassan ya bayyana cewar ministan yayi fama da rashin lafiya amma ba tare da Karin bayani akai ba.

Tawagar gwamnatin Sudan dake Juba domin halartar taron tace Janar Omar ya rasu ne da misalign karfe 2.30 na safiyar laraba sakamakon bugun zuciya.

An haifi Omar a shekarar 1960 kuma an nada shi a mukamin minister ne bayan da soji suka yiwa shugaba omar Hassan al Bashir juyin mulki a watan Afrilun bara.

Kafin nada shi minista ya rike mukamin shugaban kwamitin tsaro da na gwamnatin rikon kwarya kaan ya rike shugaban rundunar liken asiri lokacin mulkin shugaba al-Bashir tsakanin shekarar 2017 zuwa 2019.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI