Afrika

Uhuru Kenyatta ya kafa dokar hana fitar dare

Uhuru Kenyatta Shugaban kasar Kenya
Uhuru Kenyatta Shugaban kasar Kenya PSCU .jpg

Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta ya kafa dokar hana fitar dare da zummar dakile yaduwar cutar coronavirus, inda ya bayyana rage albashin sa da kuma zabtare harajin domin bunkasa tattalin arzikin kasar.

Talla

A jawabin da ya yiwa al’ummar kasar, Kenyatta yace daga ranar juma’a mai zuwa kowa zai zauna a gida daga karfe 7 na dare zuwa karfe 5 na asuba, amma banda ma’aikatan lafiya da kuma wadanda ayyukan su ya zama wajibi.

Kenyatta ya bayyana shirin rage haraji ga mutanen dake karbar albashi kasa da Dala 226, yayin da ya bayyana Dala miliyan 94 domin kula da dattijai da marayu da mabukata domin rage musu radadin halin da ake ciki.

Shugaban ya kuma bukaci dakatar da biyan bashin banki, yayin da ya baiwa ma’aikatu da hukumomin gwamnati umurnin biyan bashin Dala miliyan 122, bayan ware kusan Dala miliyan 9 da rabi wajen bunkasa harkar kula da lafiya.

Kenyatta dake daukar albashin Dala 15,000 kowanne wata, ya sanar da rage kashi 80 na albashin sa tare da na mataimakin sa, yayin da ministocin sa zasu rage kashi 30.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.