Najeriya

Matatun man Najeriya sun lakume sama da Naira biliyan 218 a 2019

Shelkwatar kamfanin man fetur na Najeriya, NNPC a Abuja.
Shelkwatar kamfanin man fetur na Najeriya, NNPC a Abuja. REUTERS/Afolabi Sotunde/File Photo

Matatun man Najeriya da ke karkashin kulawar kamfnin man fetur na kasa sun lakume jimillar kudi da ya kai Naira biliyan 218.18 a shekarar 2019.

Talla

Matatan man fetur ta Kaduna, Portharcourt da Warri, wadanda kasar ba ta cin moriyarsu a halin yanzu, gaba dayansu, sun yi asarar sama da Naira biliyan 149 a shekarar da ta gabata.

Najeriya, wacce ta fi kowace kasa a nahiyar Afrika arzikin danyen mai, ta dogara ga tatattun albarkatun man fetur da take shigowa da su daga waje, saboda matatun man ta ba sa aiki tsawon shekaru, kuma har yanzu gyara ya ci tura.

An gina matatun man da ke Kaduna da Portharcourt da Warri, ne da zummar za su tace gangunan danyen mai dubu dari hudu da arba’in da biyar, (445,000), amma a halin da ake ciki ba a cimma wannan buri da hukumomin kasar ta sanya a gaba game da su.

Alkalumma da aka samu daga shelkwatar kamfanin NNPC dake babban birnin tarayyar Najeriya Abuja a jiya Laraba, na nuni da cewa gaba daya matatun man sun samu kudin shiga da yawansu ya kai naira biliyan 68 da miliyan 96 ne a shekarar da ta gabata, amma, kuma sai suka hadu suka cinye Naira biliyan 218 da miliyan 18 a cikin shekarar.

Masu lura da al’amura a bangaren man fetur dai na ganin kamar ba za a yi kuskure ba, idan aka ce dabara ta kare wa mahukuntan Najeriya game da yadda za a gyara matatun man kasar da suka dade ba sa biyan bukatun al’ummar kasar na abin da ya shafi man fetur da dangoginsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI