Coronavirus-Duniya

Mutanen da coronavirus ta kashe a duniya sun zarce dubu 20

Wani ma'aikacin lafiya mai kula da masu cutar coronavirus a birnin Cremona na Italiya.
Wani ma'aikacin lafiya mai kula da masu cutar coronavirus a birnin Cremona na Italiya. REUTERS/Flavio Lo Scalzo

Adadin Mutanen da annobar coronavirus ko kuma COBID-19 ta kashe a duniya ya zarce 20,000 tun bayan barkewar cutar a kasar China a watan Disamban bara.

Talla

Alkaluman hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya sun ce mutane 20,599 suka mutu sakamakon wannan annoba ta coronavirus, wadda ta kama mutane 447,030 a kasashen duniya 182.

Daga karfe 7 na yammacin Talata zuwa daren jiya, mutane 2,341 suka mutu, yayin da aka samu sabbin wadanda suka kamu da cutar 43,010 a kasashen duniya.

Kasashen da mutane suka fi mutuwa n abaya bayan nan sune Spain a matsayin farko mai mutane 738, sai Italia a matsayi na biyu da mutane 683 sai kuma Faransa a matsayi na 3 da mutane 231.

Ya zuwa yanzu Italia ce ke gaba wajen adadin mutanen da suka mutu da suka kai 7,503, sai Spain mai mutane 3,434 sai China mai mutane 3,281 sai Iran mai mutane 2,077 sai kuma Faransa mai mutane 1,331.

Nahiyar Turai tafi samun adadin mutanen da suka mutu wadanda suka kai 13,824, sai Asia mai 3,596, sai Amurka da Canada mai mutane 854 sannan Gabas ta Tsakiya mai mutane 2,123.

Mutane 124 suka mutu a Yankin Amurka ta kudu da Caribbean sai Afirka mai mutane 69 sannan Yankin Oceania mai mutane 9.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.