'Yan awaren Kamarun sun tsagaita wuta saboda coronavirus
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Wani bangaren kungiyar mayakan ‘yan aware na yankin da ake amfani da harshen Ingilishi na kasar Kamaru ya sanar da tsagaita wuta kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bukata domin maida hankali kan cutar coronavirus.
Kungiyar mayakan na SOCADEF da ke fafatawa da sojojin Kamaru don kafa jamhuriyar Ambazonia ta amince da tayin na sakatare janar na MDD Antonio Guterres da cewa kasashe maso fama da yaki su tinkari cutar Covid-19 dakewa duniya barazana.
Shugaban kungiyar Ebebezer Akwanga ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, daga kasar Ghana, inda yace a shirye kungiyarsa take ta tsagaita bude huta da baiwa al’umma damar harkokin su na yau da kullum a yankin tare da mutun ta dokokin jinkai na Majalisar Dinkin Duniya.
Cikin sanarwar Akwanga ya yi kira ga shugaban kasar Kamaru Paul Biya da shima ya amsa kiran na Majalisar Dinkin Duniya, wajen kira ga sojojin sa su tsagaita wuta.
Rikici tsakanin ‘yan aware masu neman ballewa domin kafa jamhuriyar Ambazonia a yankuna biyu da ake amfani da turancin Ingilishi na Arewa maso Yamma da Kudu maso Yamma da dakarun Kamaru ya salwantar da dunbin rayuka a yankunan tare da haifar dubban ‘yan gudun hijira.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu