Bakonmu a Yau

Alhaji Idi Abdou kan farmakin Sojin Hadakar kasashen Sahel ga 'yan ta'addan yankin

Wallafawa ranar:

Sojoji sama da dubu biyar daga kasashen Faransa, Nijar da kuma Mali, sun kaddamar da wani gagarumin farmaki kan maboyar ‘yan ta’adda a kusurwar da ta hada iyakokin Mali, Nijar da Burkina, inda suka kashe ‘yan ta’adda masu tarin yawa.Sanarwa daga ma’aikatar tsaron Faransa, ta ce farmakin wanda aka gudanar daga ranar 3 zuwa 23 ga wannan wata na Maris, ya hada dakaru kusan dubu 5, wato dubu 1 da 700 daga Faransa, dubu 1 da 500 daga rundunar G5-Sahel, sai kuma wasu dubu 1 da 500 daga jamhuriyar Nijar.A game da wannan batu, Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Alhaji Idi Abdou, mai bin diddigin ayyukan sojojin kasashen yammacin duniya a yankin na Sahel, ga kuma zantawarsu.

Wasu Sojin kasashen Sahel.
Wasu Sojin kasashen Sahel. RFI / Anthony Fouchard