Ana neman kashe Farfesa Didier Raoult
Farfesa Didier Raoult jami’in kiwon lafiya da ya bayyana amfani da kwayoyin Chloroquine a Faransa na fuskantar barazana,kamar dai yadda ya sheidawa jami’an tsaro a kasar.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Jami’an tsaro na gudanar da bincike domin gano mutanen dake da hannu a wannan lamari kwanaki biyar bayan wata ganawa da manema labarai da farfesa Didier Raoult, jami’in kiwon lafiyar kasar Faransa da ya bayyana cewa amfani da kwayoyin Chloroquine na warkar da cutar Coronavirus ya yi.
Farfesa Didier Raoult ya sheidawa masu bincike cewa an kira sa ranar daya ga wannan watan da muke cikin sa, aka kuma umurce shi da ya dakatar da fadar abinda bai dace, musaman amfani da Chloroquine, baya ga haka a cewar sa washe gari an aiko masa da sako ta wayar sa .
Wasu daga cikin jaridun kasar Faransa sun ruwaito halin da ake ciki yanzu haka, Jaridar Canard Enchaine a nata bangaren ta wallafa cewa Farfesa Didier Raoult ya shigar da kara da cewa ana neman hallaka shi da kuma kokarin tursasa masa,bincike da jami’an tsaron Nantes suka dau nauyi,kasancewar daga garin na Nantes aka kira sa ta waya.
Masu bincike sun gano cewa wayar da aka kira Farfesa Raoul da ita ,na daga cikin wayoyin da aka samarwa jami’an kiwon lafiya dake aiki a asibitin gwamnatin Nantes.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu