Chadi ta karawa Sojinta karfin fada aji don fatattakar Boko Haram
Gwamnatin kasar Chadi ta bayyana Yankunan ta guda biyu da ke kusa da Tafkin Chadi a matsayin sansanin yaki, inda ta baiwa shugabannin yankunan karin karfin fada aji domin mayar da martini kan mayakan boko haram da suka kashe sojojin kasar kusan guda 100 a wannan mako.
Wallafawa ranar:
A dokar kasar da shugaba Idris Deby ya rattabawa hannu, gwamnatin ta bayyana Yankunan Fouli da Kaya a matsayin dandalin yaki, bayan ta kafa dokar ta baci a cikin su.
A karkashin wannan doka, jami’an tsaro na da hurumin gudanar da bincike a cikin gidaje dare da rana da kuma hana matafiya.
Shugaba Deby ya sha alwashin mayar da martini mai karfi kan mayakan bayan ya ziyarci sansanin sojin dake Bohoma inda aka kai harin.
Ana kallon dakarun sojin Chadi a matsayin mafi karfi a Yankin Afirka ta Yamma saboda kwarewar su wajen yakar Yan ta’adda.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu