Nijar

Gwamnatin Nijar ta gana da yan kasuwa

Kasuwar sayar da kayan gwari
Kasuwar sayar da kayan gwari www.ceas.ch

A wani taron da ya gudanar a wannan mako tsakaninsa da kungiyoyin yan kasuwa,ministan kasuwancin Jamhuriyar Nijar ya bukaci yan kasuwar da su taimaka wajen ganin sun daidaita farashin abinci da kayayyaki na masarufi domin ragewa al’ummar kasar wahalhalu a dai dai wannan lokaci da suke shirye shiryen tarben azumin Ramadana.

Talla

Nijar na daga cikin kasashen da yanzu haka ke fatan ganin an samu sauki a kasuwani a lokacin Azumi,matsallar dake hana ruwa gudu yanzu haka itace cutar Coronavirus,cutar da ta janyo durkushewar tattalin arzikin kasashe.

Fargabar  tsadar kayaki a lokacin azumi ne ya sa kungiyoyin yan kasuwa a shekaru da suka gabata neman hukumomi su taimaka tareda kawo sauki ga batutuwa da suka jibanci haraji dama samar da wani tallafi na musaman ga kananan yan kasuwa a kasar ta Nijar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.