Afrika

An sace jagoran yan Adawa na Mali

Soumaila Cisse,Shugaban yan adawar kasar Mali
Soumaila Cisse,Shugaban yan adawar kasar Mali MICHELE CATTANI / AFP

Gwamnatin Mali ta tabbatar da sace Shugaban babban jam’iyyar adawar kasar Soumaila Cisse, irinsa na farko da aka taba yi wa wani babban dan siyasa a kasar dake yammacin Afrika da ke fama da yaki da kungiyoyin yan ta’adda dake ikirarin jihadin musulunci.

Talla

An sace shugaban yan adawar kasar Mali Soumaïla Cissé ne a lokacin da yake tsakiyar yakin neman zaben yan majalisar dokoki da ake shirin gudanarwa a ranar lahadi 29 ga wannan watan da muke cikin sa.

Soumaïla Cissé, mai shekaru 70 da haihuwa a duniya wanda sau uku jere ga juna yana neman mukamin shugabancin kasar, a ranar larabar da ta gabata ne wata tawagar mutane sama da 12 dake cikin mota kirar Hilux suka sace shi a mazabarsa ta Niafounké, dake cikin yankin Tombouctou. Bayan da suka kashe mai tsaron lafiyarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.