Coronavirus

Yawan mutanen da suka kamu da Coronavirus a Amurka ya zarce na China

Wani jami'in kiwon lafiya na gudanar da gwaji don gano mutanen dake dauke da Coronavirus
Wani jami'in kiwon lafiya na gudanar da gwaji don gano mutanen dake dauke da Coronavirus ONESPHORE NIBIGIRA / AFP

Kasar China ta sake kirga sabin mutane 55 da suka kamu da cutar Covid-19, 54 daga cikinsu kuma sun doko ta ne daga kasashen waje, a dai dai wannan lokaci da kasar ke shirin rufe iyakokinta tare rage yawan kai kawon jiragen saman kasashen Duniya a kasar.

Talla

A karo na farko a cikin kwanaki 3 mutum guda ne aka gano ya harbu da cutar a cikin kasar kamar yadda sakamakon hukumomi ya nuna.

Sakamakon yawan mutanen da suka rasa rayukansu sanadiyar cutar covid 19 a Duniya yanzu haka sun haura mutane dubu 23.

A jiya Alhamis kasar Amruka ce ta fi kirga sabin wadanda suka kamu da cutar fiye da sauran kasashen Duniya inda ta dara china da Italiya

Yanzu haka dai kimanin mutane dubu 83 ne suka harbu da cutar a Amurka, wanda yasa ta zarta kasashen China da Italiya, inda a china ake da mutane dubu 81 italiya kuma dubu 80 kamar yadda wata kididiga da kamfanin dillancin labaran Faransa na Afp ya ruwaito.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI